KMT ya sake jaddada ƙudurinsa na kawo ci gaba mai ɗorewa a Yobe

0
190
KMT ya sake jaddada ƙudurinsa na kawo ci gaba mai ɗorewa a Yobe
Alhaji Kashim Musa Tumsah MFR

KMT ya sake jaddada ƙudurinsa na kawo ci gaba mai ɗorewa a Yobe

Shahararren mai taimakon jama’a da tallafa wa gajiyayyu, Alhaji Kashim Musa Tumsah MFR, ya sake jaddada aniyarsa na tallafawa ci gaban jihar Yobe, tare da mayar da hankali kan harkar ilimi, taimakon matasa, kiwon lafiya da kuma rage raɗaɗin talauci.

Tumsah ya bayyana haka a wajen gabatar da kasafin kuɗi na jihar Yobe na shekarar 2026. Tumsah ya bayyana cewa shirye-shiryensa na tallafi suna da nufin ɗaga darajar al’umma da kuma cika gurbin manufofin ci gaba na gwamnatin jiha.

KU KUMA KARANTA: KMT ya bawa kowace ɗaya daga cikin gwarazan gasar turanci ta duniya Naira dubu 500 da kwamfuta (Hotuna)

Ya jaddada cewa harkar ilimi ita ce wadda zai fi bawa fifiko na farko, yana mai bayyana ta a matsayin ginshiƙin ci gaba mai ɗorewa. Tumsah ya bayyana shirin faɗaɗa ayyukansa a yanzu wanda suka haɗa da ba da tallafin karatu, gyaran makarantu da raba kayan koyon karatu, musamman a yankunan karkara da ke fama da koma baya.

Baya ga ilimi, Tumsah ya kuma nuna ƙudurinsa na inganta ayyukan kiwon lafiya da kuma ƙarfafa matasa wajen samun sana’o’i, domin daidaita da tsarin bunƙasa tattalin arziƙin jihar baki ɗaya.

Tumsah ya samu gagarumar tarba da goyon baya daga ɗaruruwan masu ƙaunarsa da suka raka shi, alamar irin ƙima da karɓuwa da yake da ita a matsayin ɗan gwagwarmaya na gaske wajen ci gaban al’umma a jihar Yobe.

-Ibraheem El-Tafseer

Leave a Reply