Kotu ta tsige ɗan majalisar Zamfara saboda sauya sheƙa daga PDP zuwa APC
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta tsige dan majalisa Abubakar Gummi, wanda ke wakiltar mazabar Gummi/Bukkuyum ta jihar Zamfara, saboda sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC.
Mai shari’a Obiora Egwuatu ne ya yanke hukuncin, inda ya ce sauya shekar Gummi ya sabawa kundin tsarin mulkin kasa.
Kotu ta kuma hana Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ci gaba da amincewa da Gummi a matsayin dan majalisa, tare da umartar hukumar INEC da ta gudanar da sabon zabe cikin kwanaki 30.
KU KUMA KARANTA: Sulhu da ‘yan bindiga ba tare da karɓe makamansu ba, tamkar miƙa wuya ne – Gwamnan Zamfara
Hukuncin ya kuma tilasta Gummi ya mayar wa gwamnati duk albashi da alawus da ya karba tun daga 30 ga Oktoba, 2024, har zuwa ranar yanke hukuncin, tare da biyan tarar N500,000 ga PDP.
Mai shari’a Egwuatu ya soki halin ’yan siyasa na sauya sheka daga jam’iyyar da ta kai su ga nasara zuwa wata jam’iyya, yana mai cewa hakan “ba daidai ba ne doka da ɗabi’a.”









