No menu items!

Sample Page Title

Date:

Kotu a Kano ta tura matashin da ake zargi da kashe mahaifinsa gidan gyaran hali

Daga Jameel Lawan Yakasai

Babbar Kotun Jihar Kano mai lamba 7 ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Aminu Adamu ta tura wani matashi mai suna Aminu Ismail, ɗan asalin garin Ganbai a Karamar Hukumar Ajingi, zuwa gidan yari bisa zargin kashe mahaifinsa, Dahiru Ahmad.

Lauyan Gwamnati mai gabatar da ƙara, Barista Lamido Abba Sorondinki, ne ya roƙi kotu ta karanta wa wanda ake tuhuma tuhumar da ake masa, sai dai Aminun ya musanta.

KU KUMA KARANTA: Kotu a Kano ta tura wani matashi gidan gyaran hali, bisa zargin lakaɗa wa matar babansa duka

Kotun ta bayar da umarnin a mayar da wanda ake tuhuma gidan yari tare da ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 13 ga watan Nuwamba 2025 domin fara sauraron shaidu.

Ana zargin matashin da kashe mahaifinsa saboda ya hana shi yin ƙarin aure, a watan Afrilu 2024.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...