Zargin badaƙalar kuɗaɗe: An samu tsaiko a fara sauraren shari’ar da gwamnatin Kano ta shigar akan Ganduje

0
187
Zargin badaƙalar kuɗaɗe: An samu tsaiko a fara sauraren shari'ar da gwamnatin Kano ta shigar akan Ganduje
Tsohon Gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Ganduje

Zargin badaƙalar kuɗaɗe: An samu tsaiko a fara sauraren shari’ar da gwamnatin Kano ta shigar akan Ganduje

Sauraron shari’ar tsohon Gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, da wasu mutum bakwai, kan zargin cin hanci da almundahana, ya samu tsaiko a Babbar Kotun Jihar Kano a ranar Litinin.

An dakatar da zaman ne bayan wadanda ake tuhuma suka kasa mika takardunsu na bukatun su da ake bukata kafin ci gaba da shari’ar.

Gwamnatin Jihar Kano ce ta shigar da karar mai kunshe da tuhuma 11 da suka hada da cin hanci da hada baki, da karkatar da kudaden gwamnati.

KU KUMA KARANTA: Hukumar yaƙi da cin-hanci ta jihar Kano ta fara binciken Ganduje kan zargin karkatar da Naira biliyan 4 a Kano

Cikin wadanda ake tuhuma tare da Ganduje akwai matarsa Hafsat da dansa Umar, da wasu kamfanoni da mutane hudu.

Mai shari’a Amina Adamu Aliyu ta umurci dukkan bangarorin da su kammala shigar da takardunsu kafin zaman gaba, sannan ta dage shari’ar zuwa 26 ga Nuwamba, 2025.

Leave a Reply