Tsaron jihar Zamfara shi ne babban buri na – Gwamna Lawan

0
167
Tsaron jihar Zamfara shi ne babban buri na - Gwamna Lawan
Gwamna Dauda Lawal na Zamfara

Tsaron jihar Zamfara shi ne babban buri na – Gwamna Lawan

Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya bukaci masu ruwa da tsaki da su kara kaimi wajen kawo karshen ‘yan bindiga da satar mutane, da kuma matsalar rashin tsaro gaba ɗaya a jihar.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Sulaiman Idris, mai magana da yawun gwamnan, ya fitar a Gusau a yau Litinin.

KU KUMA KARANTA: Gwamnan Zamfara ya ƙaddamar da motocin bas 50 don sauƙaƙa zirga-zirga a al’ummar jihar 

Gwamna Lawal ya yi wannan kiran ne a yayin da yake jagorantar taron majalisar zartaswa karo na 18 a fadar gwamnatin jihar da ke Gusau.

Ya bayyana cewa kare jihar daga ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane da sauran nau’o’in rashin tsaro na daga cikin manyan muhimman abubuwan da gwamnatinsa ta fi bai wa muhimmanci, tare da jaddada cewa harkar tsaro hakkin kowa ne a matsayin dan kasa ko shugaba a wani mataki.

A taron na majalisar, an tattauna muhimman batutuwa da suka shafi tsaro, ilimi, lafiya, da ci gaban ababen more rayuwa, da sauransu.

Leave a Reply