An yi taron ranar makarantu masu zaman kansu a Potiskum

0
177
An yi taron ranar makarantu masu zaman kansu a Potiskum

An yi taron ranar makarantu masu zaman kansu a Potiskum

Ranar Litinin da ta gabata (13/10/2025) ita ce ranar makarantu masu zaman kansu a Najeriya. A garin Potiskum an gudanar da bukin murnar zagayowar wannan rana, inda makarantu masu zaman kansu sama da 46 suka halarci taron bukin, da ya gudana a harabar makarantar St’ Peter’s Academy and College Potiskum jihar Yobe.

An fara taron ne da misalin ƙarfe 10:00 na safe, har zuwa ƙarfe 1:00 na rana. Makarantu sama da 20 ne suka gabatar da wasanni iri daban-daban a wajen. Sun yi shigar kaya na gargajiya na yaruka daban-daban, irinsu Fulani, Ibo, Yoruba da Hausa.

Sannan an gudanar da muƙala (presentation) a tsakanin makarantun da suka halarci taron, cikin harshen Turanci da Larabci. Wasu makarantun kuma sun nuna kayayyakin da ɗalibansu suka ƙera da hanunsu (skills acquisition), irin su Fanka, Buta da ɗinki na kayan sakawa (Tailor).

A jawabinsa, shugaban makarantu masu zaman kansu na Potiskum, Malam Muhammad Sambo Adamu, ya bayyana irin ci gaba da aka samu da ɗimbim nasarori a shekaru 2 da ya yi yana gudanar da shugabancin makarantu masu zaman kansu a Potiskum.

KU KUMA KARANTA: Hukumar NEDC ta ƙaddamar da Makarantar Mega ta zamani a Potiskum (Hotuna)

Malam Muhammad Sambo ya yi godiya ga Gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni kan irin nuna goyon baya da yake yiwa makarantu masu zaman kansu. Sannan ya yi godiya ga ma’aikatar ilimi ta jihar Yobe da ta ƙaramar hukumar Potiskum, saboda irin haɗin kai da suke ba su a duk lokacin da suka zo musu da buƙata.

Jama’a da dama ne suka halarci wajen taron, ciki sun haɗa da wakiliyar ma’aikatar ilimi ta jihar Yobe, Hajiya Fatima, da wakilin Education Secretary na ƙaramar hukumar Potiskum, wakilin ‘Yansanda, wakilin DSS, wakilin NSCDC da shugabannin makarantu masu zaman kansu (private school proprietors) da dama.

Shugaban makarantar St’ Peter’s Academy and College Potiskum, Venerable Thomas Y. Sankwi, shi ne ya yi jawabin ƙarshe kuma ya rufe taron da addu’a.

Leave a Reply