Shugaban hukumar zaɓe ta jihar Yobe, Dakta Mamman Mohammed ya rasu
Shugaban hukumar zaɓe ta jihar Yobe (YOSIEC), Dakta Mamman Mohammed (Shamakin Fika) ya rasu.
Ɗansa, Barista Abba Mamman ne ya tabbatar da rasuwarsa.
Dakta Mamman ya rasu ne a asibitin koyarwa na jami’ar jihar Yobe da ke Damaturu, bayan ya yi fama da doguwar jinya.
KU KUMA KARANTA: Marigayi Alhaji Aminu Dantata ya bar mana wasiyar a binne shi a Madina idan ya rasu – Inji iyalansa
Kafin rasuwarsa shi ne shugaban hukumar zaɓe ta jihar Yobe (YOSIEC), sannan shi kwararren likita ne (Medical Doctor), sannan kuma ya riƙe kwamishinan lafiya na jihar Yobe a lokacin mulkin Bukar Abba Ibrahim.
Dakta Mamman ya rasu yana da shekaru 74, ya bar mata 3 da ‘ya’ya 33 rayayyu.
Za a yi jana’izarsa gobe Talata da misalin ƙarfe 1:30 na rana a fadar mai martaba Sarkin Fika da ke Potiskum.









