Marigayi Alhaji Aminu Dantata ya bar mana wasiyar a binne shi a Madina idan ya rasu – Inji iyalansa

0
102
Marigayi Alhaji Aminu Dantata ya bar mana wasiyar a binne shi a Madina idan ya rasu – Inji iyalansa

Marigayi Alhaji Aminu Dantata ya bar mana wasiyar a binne shi a Madina idan ya rasu – Inji iyalansa

Iyalan marigayi Alhaji Aminu Alassan Dantata sun shaida cewa marigayin ya bar musu wasiyar cewa duk lokacin da ya rasu a binne gawarsa a birnin Madina.

Daya daga cikin iyalansa kuma yar uwa ga uwar gidan marigayin wadda ta rasu shekaru biyu da suka gabata Hajiya Amina Umar Fulani ce ta shaida hakan da safiyar yau Asabar.

Tace marigayin ya bada wannan wasiyar ne tun bayan rasuwar matarsa marigayiya Hajiya Rabi Tajo Dantata a Madina a kuma binneta a birnin na Madina.

KU KUMA KARANTA: Fitaccen ɗan kasuwa a Najeriya Alhaji Aminu Ɗantata ya rasu

Tun safiyar yau Asabar Shugaban majalisar Malamai ta Kano Shiekh Ibrahim Khalil ya sanar da cewa za’ayi sallar Ga’ib ga marigayi Alhaji Aminu Dantata a masallacin Juma’a na Aliyu Bin Abi Dalib dake Dangi a birnin Kano da karfe 2 na rana.

Ya rasu a Dubai daga nan za’a dauki gawarsa zuwa birnin Madina domin binne gawarsa a kusa da uwar gidansa.

Leave a Reply