Kotu ta ba da umarnin kama tsohon Shugaban hukumar zaɓe, Farfesa Muhmud Yakubu

0
234
Kotu ta bada umarnin kama tsohon Shugaban hukumar zaɓe, Farfesa Muhmud Yakubu
Mahmud Yakubu, tsohon shugaban INEC

Kotu ta ba da umarnin kama tsohon Shugaban hukumar zaɓe, Farfesa Muhmud Yakubu

Daga Jameel Lawan Yakasai

Wata kotun tarayya dake zaman ta a Osogbo dake jihar Osun ta bawa babban Sifeton ƴan sanda Nijeriya Kayode Egbetokun umarnin kama tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC Farfesa Mahmud Yakubu kan abinda ta ambata da raina kutu.

Wannan na zuwa ne bayan da farfesa Yakubu Mahmud ya rubuta takardar barin aikin bayan karewa wa’adin a shugabancin hukumar.

KU KUMA KARANTA: Shugaban hukumar zaɓe ta ƙasa INEC Mahmood Yakubu ya sauka daga kujerarsa 

Tun da fari dai Jam’iyyar Action Alliance ce ta shigar da kara gaban kotun domin kalubalantar hukumar zaben da shugabanta Farfesa Yakubu, bisa kin yin amfani da hukuncin kotu kan karar mai lamba FHC/OS/CS/194/2024 wadda mai shari’a Funmilola Demi-Ajayi ta yanke.

Leave a Reply