Gwamna Zulum ya ba da kauytar gida a ma’aikaciyar lafiya da ta shafe shekaru 20 tana aiki a Borno

0
154
Gwamna Zulum ya ba da kauytar gida a ma'aikaciyar lafiya da ta shafe shekaru 20 tana aiki a Borno
Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Zulum

Gwamna Zulum ya ba da kauytar gida a ma’aikaciyar lafiya da ta shafe shekaru 20 tana aiki a Borno

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya baiwa wata ma’aikaciyar lafiya, Marbel Ijeoma Duaka kyautar gida.

Daily Trust ta rawaito cewa, ɗan matar mai suna Anthony, wanda ya kammala karatu a fannin ilimin Banki da Kudi, ya samu aiki a Jami’ar Kashim Ibrahim da gwamnatin jiha ke da ita a Maiduguri.

Yayin da ya ke mika mata makullin gidan, gwamnan ya ce Duaka, ƴar asalin jihar Anambra ta dade tana aiki a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Farko da ke Mafa fiye da shekaru ashirin, kuma bata taba barin garin duk da lokacin da rikicin Boko Haram ya yi tsanani.

KU KUMA KARANTA: Zulum ya bawa jami’an tsaro kyautar gidaje da motoci a jihar Borno

Duaka na cikin malamai da ma’aikatan lafiya 72 da suka samu kyautar sabbin gidaje a wani biki da gwamnan ya kaddamar a karamar hukumar Mafa, ranar Talata.

A tunawa, a watan Oktoba 2022, Zulum ya ba wata malama, Ibo daga Jihar Abia, Misis Obiageli Mazi, gida a matsayin lada saboda jajircewa da halin kishi da ta nuna bayan shekaru 31 tana aiki a Jihar Borno.

Leave a Reply