Tattalin arziƙin Najeriya na ƙara haɓaka a ƙarƙashin mulkin Tinubu – Akume

0
208
Tattalin arziƙin Najeriya na ƙara haɓaka a ƙarƙashin mulkin Tinubu - Akume
Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume

Tattalin arziƙin Najeriya na ƙara haɓaka a ƙarƙashin mulkin Tinubu – Akume

Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, ya bayyana kwarin gwiwa game da makomar Najeriya, yana mai cewa tattalin arzikin ƙasar na kara habaka a ƙarƙashin mulkin Shugaba Bola Tinubu.

Ya bayyana haka ne yayin bikin kaddamarwa da naɗin shugabanni na ƙungiyar Shugabannin Addinin Kirista na Arewacin Najeriya (NOCRELA), a Abuja a ranar Alhamis.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa (NAN) ya ruwaito cewa taken taron shi ne: “Rawar da Shugabannin Kirista za su taka wajen Gina Ƙasa.”

KU KUMA KARANTA: Tinubu ya janye dokar-ta-ɓaci a jihar Ribas, ya umarci Fubara ya dawo aiki

Akume ya ce bunƙasar da tattalin arziki daga kayan da ake ganewa a cikin kasa (GDP) da adadin ajiyar kuɗaɗen ƙasar na ƙasashen waje (foreign reserves) na samun ci gaba. A cewarsa, GDP ya kara habaka da kashi 4.4%, kuma ajiyar kuɗin waje ta kai dala biliyan 42.

Ya kuma yi kira da a samu haɗin kai tsakanin ‘yan Najeriya, yana jaddada yadda Shugaba Tinubu ke iya aiki tare da mutane masu addinai da ra’ayoyi daban-daban.

Leave a Reply