Tinubu yana so a yi zaɓe na gaskiya a 2027 – Kakakin Majalisar Tarayya Abbas
Kakakin Majalisar Wakilai ta Tarayya, Rt. Hon. Tajudeen Abbas, ya bayyana cewa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙuduri aniyar tabbatar da gudanar da zaɓen 2027 cikin gaskiya da inganci.
Da yake jawabi a ranar Alhamis, Abbas ya ce majalisar dokoki ta ƙasa ta riga ta fara aikin gyara dokar zabe ta 2022 Electoral Act, domin ƙarfafa gaskiya, rikon amana da kuma ingancin zabubbuka a nan gaba.
KU KUMA KARANTA: Yawaitar bashin da Najeriya ke karɓowa abin damuwa ne – Tajuddeen Abbas
A cewarsa, gyare-gyaren za su shafi guraben da ake gani a cikin dokar, musamman a bangaren amfani da fasahar zamani, tura sakamakon zabe, da kuma sa ido kan ayyukan jam’iyyun siyasa.
“Shugaba Tinubu ya kuduri aniyar barin tsarin zabe da ‘yan Najeriya za su amince da shi. Wannan ne ya sa muke aiki tare da bangaren zartarwa domin tabbatar da cewa an gyara dokar zabe ta 2022 don inganta gaskiya da amana kafin zaben 2027,” in ji Abbas.
Ya kara da cewa majalisar na da niyyar tabbatar da sauye-sauye da za su dawo da amincewar jama’a ga tsarin dimokuradiyya na kasarnan.









