Cikar Najeriya shekaru 65: Jonathan ya hori ‘yan ƙasar da ka da su fidda rai da samun ci gaba

0
217
Cikar Najeriya shekaru 65: Jonathan ya hori 'yan ƙasar da ka da su fidda rai da samun ci gaba
Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan

Cikar Najeriya shekaru 65: Jonathan ya hori ‘yan ƙasar da ka da su fidda rai da samun ci gaba

Tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, ya roki ‘yan Najeriya da kada su yanke ƙauna duk da ƙalubalen da ake fuskanta a yanzu, sai dai su ci gaba da riƙe fata a kan manyan damarmaki da ke cikin ƙasar.

Jonathan ya bayyana hakan ne a cikin saƙon taya murna ga ‘yan Najeriya a bikin cikar ƙasar shekaru 65 da samun ‘yancin kai.

Saƙon ya fito ne daga hannun mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Mista Okechukwu Eze, a Abuja ranar Laraba.

A cewar Jonathan, bikin ranar ‘yancin kai na ba da dama ga Najeriya ta waiwayi tafiyarta ta gina ƙasa, ciki har da ƙalubalen da aka fuskanta da kuma manyan damarmaki da ke gaba.

KU KUMA KARANTA: Siyasar Najeriya cike take da mayaudara da masu cin amana — Jonathan

“Najeriya ƙasa ce mai albarka, wadda Allah ya ba da yalwar ƙasa, albarkatun ƙasa, kuma sama da komai, basira da ƙirƙira na al’umma.

“Dumbin al’adunmu da iliminmu da hikimarmu sun ci gaba da bambanta ‘yan Najeriya a kowane fage na rayuwar ɗan adam, a gida da wajen ƙasa.”

Jonathan ya shawarci ‘yan Najeriya da su bar kishin ƙasa ya jagoranci ayyukansu.

Leave a Reply