Ba za mu bari jihar Kwara ta zama mafakar ‘yan bindiga ba – Gwamna Abdulrazaq
Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya ce gwamnatinsa ba za ta bari ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane su samu mafaka a jihar ba.
Gwamnan ya fadi haka ne bayan harin da aka kai karamar hukumar Oke-Ode, Ifelodu inda aka kashe mutane da dama.
A cewarsa, ya riga ya sanar da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu tare da neman ƙarin jami’an tsaro a yankunan kan iyaka.
KU KUMA KARANTA: Wata matar aure a jihar Kwara ta mutu sakamakon fashewar iskar gas
AbdulRazaq ya bayyana cewa an riga an kaddamar da farmaki tsakanin Soja da DSS da ƴan sanda a kan iyakar Kwara–Kogi, inda aka kashe akalla ‘yan bindiga 15.
Ya ce rundunar soji ta sauya wurin zama na GOC Division ta 2 zuwa Ilorin domin ƙara tsaurara matakan tsaro.
Ya kara da cewa gwamnati za ta ci gaba da tallafa wa hukumomin tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a, tare da gargadin cewa duk wani mai laifi da ke neman tada hankalin al’umma ba zai tsere wa hukunci ba.









