Wata matar aure a jihar Kwara ta mutu sakamakon fashewar iskar gas

1
293

Fashewar iskar gas da ta afku a safiyar ranar Litinin a Omu-Aran, hedkwatar ƙaramar hukumar Irepodun ta jihar Kwara, ta yi sanadin mutuwar wata matar aure mai suna Misis Adeola Adewale.

A cewar hukumar kashe gobara ta jihar, lamarin ya faru ne a Unguwar Tabernacle 2c, garejin Egbe a cikin Omu-Aran, a lokacin da matar ke shirya wa iyalinta abinci.

Sai dai mijin matar, wanda shi ma ya maƙale ya kasa fita saboda gobarar, ya samu kuɓuta ne bayan da ɗaukin gaggawa da ‘yan kwana-kwana suka kai masu.

Mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar, Hassan Adekunle, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce “fashewar iskar gas ta yi sanadiyar ƙonewar ginin yayin da ɗakin dafa abinci da ɗakin cin abinci suka ƙone ƙurmus.

Ya ce ‘yan kwana-kwana sun kai mijin matar, da shi ma ya samu munanan raunuka zuwa asibiti inda yake jinya.

Adekunle ya ce daraktan hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kwara, Prince Falade Olumuyiwa, ya buƙaci jama’a musamman mata da su je su koyi ingantacciyar hanyar amfani da silindar gas na girki.

1 COMMENT

Leave a Reply