PDP a tsaye take ƙyam tana jiran zaɓen 2027 – Gwamna Fintiri
Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa ya bayyana cewa jam’iyyar PDP ta sake tsari kuma ta shirya tsaf don fuskantar babban zaben shekarar 2027.
Fintiri, wanda ya yi magana da manema labarai a wajen babban taron jam’iyyar na jiha da aka gudanar a Yola, ya ce an gudanar da taron cikin gaskiya da adalci, lamarin da ya nuna karfin gwiwar jama’a a jam’iyyar.
KU KUMA KARANTA: Zaɓen 2027: PDP ta ware kujerar takarar shugaban ƙasa a yankin Kudancin Najeriya
Ya kuma tabbatar da cewa sabbin shugabannin da aka zaba za su jagoranci jam’iyyar cikin kwarewa na tsawon shekaru hudu masu zuwa.
A cewar gwamnan, gwamnati da jam’iyyar na aiki kafada da kafada domin faranta ran al’umma da kuma samar da kyakkyawan shugabanci.
Shi ma Golfa Mallim, wacce ta nemi kujerar majalisar wakilai ta Guyuk/Shelleng, ta taya sabbin shugabannin murna, tare da bayyana sabon shugaban jam’iyyar a jihar, Alhaji Hamza Madagali, a matsayin jagora mai kishin jama’a da hangen nesa.
Ta ce jagorancinsa zai ƙarfafa PDP wajen ƙwato kujeru da dama a babban zaben 2027.
A taron, PDP ta zabi Alhaji Hamza Madagali a matsayin Shugaban Jiha, yayin da Saleh Shelleng ya zama Sakataren jam’iyyar na tsawon shekaru hudu masu zuwa.









