Gamayyar Kotun muslunci a Kano sun buƙaci Gwamnatin Kano ta saya musu motoci ko kuɗin saye motocin
Daga Jameel Lawan Yakasai
Shugaban Ƙungiyar Alƙalan Kotunan Shari’ar Musulunci ta Kano, Alƙali Ustaz Ibrahim Sarki Yola, ya roƙi Gwamnan Jihar Kano da ya tallafa musu da motocin hawa ko kuɗin saye.
Ustaz Sarki Yola ya bayyana haka ne a lokacin ziyarar da Babban Alƙalin Alƙalai na Jihar, Dr. Tijjani Yusuf Yakasai, ya kai Kotunan Shari’ar Musulunci na Kofar Kudu.
KU KUMA KARANTA: An yi kira ga kotun ƙoli ta gaggauta yanke hukunci kan shari’ar masarautar Kano
Ya ce rashin abin hawa na sanya alƙalai cikin barazana, musamman idan aka gansu a tashar mota suna jiran ta cika kafin ta kai su wurin aiki, inda ya kuma yaba wa gwamnan bisa biyan hakkokinsu na baya.
Ustaz Yola ya jaddada cewa, sun san cewa akwai nauyi sosai a kan gwamnati amma suna roƙon a dube su, domin wasu alƙalan in sun je tasha ma alfarma su ke nema.









