Gwamnan Kano ya canza kwamishinan shari’a

0
168
Gwamnan Kano ya canza kwamishinan shari'a

Gwamnan Kano ya canza kwamishinan shari’a

Daga Jameel Lawan Yakasai

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da yi wa wasu jami’an gwamnatinsa garambawul.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya fitar, wannan mataki na daya daga cikin kokarin da ake yi na karfafa sha’anin mulki.

A cewar umarnin gwamnan, babban mai shari’a kuma kwamishinan shari’a Barr. Haruna Isa Dederi an mayar da shi ma’aikatar sufuri yayin da babban lauya kuma babban sakataren ma’aikatar Barr. Mustapha Nuruddeen Muhammad ya koma ma’aikatar muhalli don zama babban sakatare.

KU KUMA KARANTA: Abin da ya sa Gwamnan Kano ya kori hadimansa guda 2

Kwamishinan harkokin jin kai, wanda ya kasance mai rikon kwarya a ma’aikatar sufuri zai koma babbar ma’aikatarsa ta jin kai.

Gwamnan ya umurci dukkan jami’an da wannan sauyi ya shafa da su mika al’amuran ofisoshinsu ga babban jami’in ma’aikatar.

Mikawa da karbar aikin za a kammala shi nan take, wanda zai fara aiki daga gobe Talata 23 ga Satumba, 2025 kafin a rufe kasuwanci.

Leave a Reply