Naira dubu 9 kacal Ganduje ya tafi ya bari a asusun Gwamnatin Kano – Gwamna Abba Kabir Yusuf
Daga Jameel Lawan Yakasai
Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin bikin raba takardun ɗaukar aiki ga malaman BESDA 4,315 a Kano, a ranar Alhamis.
A cewar gwamna Abba Kabir Yusuf, sabuwar gwamnati ta yi nasarar farfaɗo da tattalin arzikin jihar, inda yanzu asusun ke cike da biliyoyin naira da ake amfani da su wajen jin daɗin Kanawa.
KU KUMA KARANTA: An yi sulhu tsakanin Gwamna Abba Kabir Yusuf da Sheikh Daurawa
Gwamnan ya zargi gwamnatin baya da sakaci wajen tafiyar da dukiyar jama’a, ciki har da ɗaukar masu ba da shawara kan haraji fiye da 128 .
Ya ce gwamnatinsa ta rufe dukkan hanyoyin zubar da kuɗaɗe, tana kuma tabbatar da cewa dukiyar jihar tana amfanar da al’umma.
Haka kuma, ya nuna gamsuwa da ci gaban da aka samu a jarabawar NECO ta shekarar 2025, yana mai cewa hakan ya nuna tasirin zuba jari da gwamnati ta yi a fannin ilimi.
Gwamnan ya jaddada cewa za a ci gaba da mayar da hankali kan ilimi, lafiya da ayyukan raya ƙasa, tare da kiyaye gaskiya da rikon amana duk da sukar da ke fitowa daga ‘yan adawa.









