Za a dinga koyar da yaren China a makaratun Sakandire na Najeriya – Gwamnatin Tarayya
Gwamnatin Tarayya ta sanar da saka harshen China (Mandarin) a cikin kundin karatun makarantun sakandare a Najeriya.
Sakataren Ilimi na Abuja, Dakta Danlami Hayyo ne ya bayyana hakan a Abuja yayin kaddamar da “Chinese Corner” na 14, inda ya ce wannan mataki na nuna muhimmancin harshen Mandarin a kasuwanci, ilimi, al’adu da diflomasiyya.
Ya ce koyar da ɗalibai harshen zai ba su damar gogayya a duniya tare da samun damar ilimi da kasuwanci.
KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Yobe ta haramta bukukuwan ‘Marker Day’ a dukkan makarantun Sakandire, saboda lalata tarbiyya
A cewarsa, wannan shiri wani bangare ne na ƙoƙarin gwamnati wajen shirya matasa domin zama masu iya yin gogayya a fagen duniya.
Ana ganin matakin zai kara zurfafa dangantakar Najeriya da ƙasar China a fannoni da dama, musamman ilimi da musayar al’adu.









