Malamai 35 sun zama Farfesoshi a Jami’ar Usman Ɗanfodio da ke Sakkwato 

0
345
Malamai 35 sun zama Farfesoshi a Jami'ar Usman Ɗanfodio da ke Sakkwato 

Malamai 35 sun zama Farfesoshi a Jami’ar Usman Ɗanfodio da ke Sakkwato

Majalisar Gudanarwa ta Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Spkoto (UDUS) ta amince da ɗaga matsayin malamai 35 zuwa matsayin farfesoshi.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai na jami’ar, Sama’ila Yauri, ya fitar a ranar Alhamis a Sakoto.

Yauri ya ce amincewar ta biyo bayan gabatar da sakamakon aikin tantancewa a taron majalisar na 173 da Shugaban Majalisar, Farfesa Attahiru Jega, ya jagoranta.

KU KUMA KARANTA: Miji da mata sun zama farfesoshi a lokaci guda a jami’ar Bayero

A cewarsa, malamai 21 kuma an ɗaga su zuwa matsayin “Reader”, yayin da guda huɗu aka ɗaga su zuwa matsayin Babban Malami (Senior Lecturer).

Ya ce Farfesa Jega ya bayyana gamsuwa da yadda aikin ya gudana tare da ƙarfafa dukkan malamai da ma’aikatan da aka ɗaga mukamansu su yi aiki da cikakken sadaukarwa.

Haka kuma, Shugaban Jami’ar, Farfesa Bashir Garba, ya taya su murnar samun karin girma tare da jan hankalinsu da su nuna ƙarin jajircewa a ayyukansu.

Leave a Reply