Za mu hukunta El rufa’i, ba zamu lamunta ya lalata mana zaman lafiyar Kaduna ba – Gwamnan Kaduna
Gwamnatin Jihar Kaduna ta fitar da wani gargaɗi na ƙarshe ga tsohon Gwamna Malam Nasir El-Rufai, tana tuhumarsa da shirya makirci domin tayar da rikici a jihar da nufin rushe zaman lafiya da ake samu yanzu.
A wata sanarwa da Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida, Dr. Suleiman Shuaibu, ya fitar a Kaduna, ya bayyana cewa mutanen jihar sun sha wahala, zubar da jini da rarrabuwar kawuna a baya, don haka gwamnati ba zata zuba ido ba a bar tsohon gwamnan da ya bar jihar cikin ruɗani ya sake tayar da tarzoma.
Sanarwar ta ce, El-Rufai baya iya jure ganin ci gaban da ake samu a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Uba Sani, wanda ya fito da tsare-tsaren gwamnati na haɗin kai, tsaro da ci gaban jama’a. A cikin shekaru biyu kacal, jihar Kaduna ta farfaɗo daga halin karyewar tsaro, ƙuncin tattalin arziki da rarrabuwa zuwa tafarkin cigaba da zaman lafiya.
KU KUMA KARANTA: ‘Yansanda sun gayyaci Elrufai kan zargin ta da hargitsi a Kaduna
Sai dai sanarwar ta ce, El-Rufai ya ƙara daure damara bayan shan kayen ’yan takaransa suka yi a zaɓen cike gurbi na 16 ga watan Agusta, inda aka kayar da su a zaɓe mai gaskiya da amincewar jama’a ga gwamnatin Uba Sani.
Haka nan, sanarwar ta zargi El-Rufai da gudanar da taron siyasa mai cike da rikici a ranar 30 ga watan Agusta, wanda ya haifar da tashin hankali da harbe-harbe, sannan daga baya ya zargi gwamnati da tura ’yan daba – abin da gwamnatin ta ce ƙarya ce don tayar da hankalin jama’a.
Bugu da ƙari, gwamnatin ta yi Allah-wadai da zargin da El-Rufai ya yi a gidan talabijin cewa gwamnati na “biyan kudin goro ga ’yan ta’adda wannan magana raini ce wa kokarin sojoji da jami’an tsaro, sannan tana ƙoƙarin haddasa fargaba a tsakanin al’umma. Ofishin Mai Baiwa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Tsaro (ONSA) ma ya karyata wannan zargi, ya bayyana shi a matsayin ƙarya da yaudara.
Gwamnatin ta lissafo nasarorin da aka samu a fagen tsaro da ci gaban jama’a, ciki har da kawar da shahararrun shugabannin ’yan ta’adda kamar Boderi, Baleri, Sani Yellow, Janburos, Buhari da Boka, tare da dawo da zaman lafiya a yankuna kamar Birnin Gwari, Giwa, Kajuru, Kachia, Kauru da Igabi.
Haka kuma ta bayyana irin ci gaban da gwamnatin Uba Sani ta samu a fannin ilimi, kiwon lafiya, hanyoyi da walwalar jama’a, inda ta ce yanzu fiye da mutum miliyan 2.5 da ba su da asusun banki an haɗa su da tsarin kudi, asibitoci da makarantu sun samu ingantuwa, sannan tattalin arziki ya fara murmurewa.
KU KUMA KARANTA: Majalisar jihar Kaduna za ta ɗauki mataki kan yaron El-Rufa’i
Sanarwar ta ce:
“Nasir El-Rufai mutum ne da ke jin daɗin rikici, ya saba da siyasar bayar da tsoro da rarrabuwa. Amma gwamnatin nan ba za ta lamunci hakan ba. Zaman lafiyar Kaduna abu ne da ba za a taɓa yin wasa da shi ba. Duk wanda ya yi ƙoƙarin tada fitina za a hukunta shi da ƙarfin doka.”
Gwamnatin ta yi kira ga jama’ar jihar Kaduna da su guji biyewa surutun tsohon gwamnan, su rungumi zaman lafiya da haɗin kai da gwamnati ke ginawa.
A ƙarshe, sanarwar ta ce:
“Lokacin El-Rufai ya wuce. Kaduna ta zabi zaman lafiya da ci gaba. Ba za mu bar kowa ya mayar da jihar baya ba.”









