Wanene Farfesa Hafiz Miko Yakasai na Jami’ar Bayero?
Daga Jameel Lawan Yakasai
Farfesa a sashin nazarin harsuna na jami’ar Bayero Farfesa Hafiz Miko, ya rasu a daren jiya Alhamis.
Kafin rasuwarsa, Farfesa Miko Yakasai shine a matsayin Provost na farko na sabuwar Kwalejin Harsuna da Al’adun Dan Adam, abin da ya nuna irin jajircewar sa da sadaukar da rayuwarsa wajen bunƙasa ilimi da bincike.
Farfesa Miko ya yi suna wajen bada muhimmiyar gudummawa ga nazarin harsunan Najeriya da fannin al’adu, inda ya bar gado da za ta ci gaba da zama abin koyi ga masu zuwa.
KU KUMA KARANTA: Farfesa Hafizu Yakasai na jami’ar Bayero ya rasu
Tuni aka yi jana’izar sa da safiyar yau Juma’a a unguwar Yakasai.
Shugabannin jami’ar BUK, ciki har da Shugaban Majalisar Koli, Shugaban Jami’a, Majalisar Gudanarwa da Ma’aikata tare da dalibai, sun mika ta’aziyyarsu ga iyalansa, abokai da al’umma baki ɗaya da ya yi tasiri a rayuwarsu.









