Gwamnatin sojin Burkina Faso ta haramta auren jinsi

0
119
Gwamnatin sojin Burkina Faso ta haramta auren jinsi
Shugaban Sojin Burkina Faso, Ibrahim Traore

Gwamnatin sojin Burkina Faso ta haramta auren jinsi

Gwamnatin sojin Burkina Faso a ƙarƙashin jagorancin Faso Ibrahim Traore ta sanar da haramta auren jinsi a ƙasar baki ɗaya.

Wannan na zuwa ne kimanin shekara guda bayan an amince da wani daftarin dokoki da aka yi garambawul a kan dokokin iyalin ƙasar, inda a ciki aka ƙara auren jinsi.

BBC Hausa ta ruwaito cewa ƙasar da ke yankin Sahel ta kasance a cikin ƙasashen Afirka 22 a cikin 54 da suka amince da auren jinsi, lamarin da ke ɗaukar hukuncin kisa ko zaman gidan kaso mai tsaro a wasu ƙasashen.

KU KUMA KARANTA: Burkina Faso ta kori wasu sojoji 14 daga aiki

A jiya Litinin ne gwamnatin ƙasar ta amince da sabuwar dokar wadda ta haramta auren na jinsin.

A sabuwar dokar, wanda aka kama da auren jinsi zai iya fuskantar zaman gidan yari na shekara biyar, kamar yadda ministan shari’a na ƙasar Edasso Rodrigue Bayala ya sanar a kafar gwamnatin ƙasar ta RTB.

A bara ma dai maƙwabciyar ƙasar, Mali ta yi dokar haramta auren jinsi.

Ko zuwan Rasha Afirka ya inganta tsaro a yankin Sahel?

Leave a Reply