Matan jihar Yobe uku sun kafa tarihi a Najeriya 

0
275
Matan jihar Yobe uku sun kafa tarihi a Najeriya 
Farfesa Halima Gambo, Aisha Umar Bubaram da Farfesa Hadiza Hamma

Matan jihar Yobe uku sun kafa tarihi a Najeriya

A yau, Jihar Yobe ta samu manyan fitattun mata guda uku daga garin Potiskum waɗanda suka kafa tarihi a Najeriya.

1. Aisha Umar Bubaram

Mace ta farko daga Arewacin Najeriya da ta kai matsayin Babbar Jami’a a tarihin shekara 131 na Bankin FirstBank

Aishatu Bubaram ‘yar asalin Jihar Yobe, ‘ya ga Mai Martaba Sarkin Potiskum, Alhaji Umaru Bubaram Ibn Wuriwa Bauya I, OON, ta yi fice a matsayin ƙwararriyar shugabar harkokin kuɗi wacce aikinta ya haɗa da nagarta, jajircewa da jagoranci na sauyi. Bayan ta shafe sama da shekaru 25 tana aiki a ɓangaren banki, a halin yanzu tana riƙe da muƙamin Group Executive a FirstBank of Nigeria Limited, kuma tana daga cikin Non-Executive Directors a hukumar FirstBank Guinea.

Hawan ta daga matsayin matashiyar ma’aikaciyar horo (Graduate Trainee) zuwa samun shugabancin zartarwa ya kasance labarin jajircewa da himma. Abin tarihi shi ne cewa ta zama mace ta farko daga Arewacin Najeriya da ta kai matsayin Babbar Jami’a a tarihin shekara 131 na FirstBank.

KU KUMA KARANTA: Jihar Yobe ta shiga cikin kasuwannin duniya a harkar kasuwanci

Baya ga harkar Banki, ita ce ta kafa ‘Hearty Hands Humanity Foundation’, ta hanyar wannan ƙungiya take fafutukar tabbatar da samun ilimi da kiwon lafiya ga al’ummomin da ke cikin ƙalubale a faɗin Najeriya. Ƙoƙarin jin-ƙai da ayyukan alherinta sun ci gaba da shafar rayuka da dama

2. Farfesa Halima Gambo

Farfesa Halima Gambo, ta kafa tarihi a matsayin mace ta farko a Najeriya da ta zama Farfesa a fannin ilimi da binciken cututtukan dabbobi (Veterinary Pathology).

Ta fara aikin koyarwa a shekarar 2004 a Jami’ar Maiduguri, inda ta ci gaba da yin bincike, koyarwa da jagoranci har zuwa samun matsayin Farfesa.

KU KUMA KARANTA: Shugaba Tinubu ya taya gwaraza ‘yan jihar Yobe da suka lashe gasar turanci a Landan murna

Baya ga aikin jami’a, tana riƙe da manyan muƙamai kamar:

Mataimakiyar Shugaba ta ƙasa, na Veterinary Council of Nigeria (VCN)

Shuguwar NVMA, reshen Jihar Borno

Mataimakiyar Darakta, University of Maiduguri Business School (UMBS).

3. Farfesa Hadiza Hamma: Itama ‘yar asalin garin Potiskum ce kuma, Kuma mace ta farko daga Arewa maso Gabas mai ƙaramin shekaru da ta zama Farfesa a Law . Malama ce a jami’ar Abuja.

Dukkaninsu ‘yan asalin garin Potiskum ne, Aisha Umar Bubaram da Farfesa Halima Gambo ‘yan ƙabilar Ngizim, Farfesa Hadiza Hamma kuma ƙabilar Bolewa. Wannan nasara ta ƙara nuna cewa Yobe na taka muhimmiyar rawa wajen fitar da manyan mata masu tasiri a harkar ilimi da kasuwanci a Najeriya.

Leave a Reply