MƊD ta amince da ci gaba da shirin wanzar da zaman lafiya a Lebanon
Kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ya kaɗa ƙuri’ar amincewa da tsawaita aikin dakarun kiyaye zaman lafiya a kudancin Lebanon har zuwa ƙarshen shekarar 2027.
An gabatar da shawarar janye dakarun na UNIFIL bayan da Amurka ta yi barazanar yin amfani da ikonta idan aka tsawaita aikin ba tare da ƙayyade wa’adin ƙarshe ba.
KU KUMA KARANTA: Muna fatan Kano ta kece sa’a a ɓangaren Ilimi, kiwon lafiya da noma kafin 2030 – MƊD
Amurka da Isra’ila sun daɗe suna fafutikar ganin an janye dakarun UNIFIL, an kuma miƙa alhakin tsaron ga gwamnatin Lebanon.
Dakarun UNIFIL na gudanar da sintiri a kan iyakar kudancin Lebanon tun bayan mamayar Isra’ila a shekarar 1978, sai dai masu suka na cewa ta gaza wajen rushe ƙungiyar Hezbollah.









