Ribar da muke samu ta ragu da kashi 79% a watan Yuli – NNPC

0
146
Ribar da muke samu ta ragu da kashi 79% a watan Yuli - NNPC

Ribar da muke samu ta ragu da kashi 79% a watan Yuli – NNPC

Kamfanin Mai na Ƙasa (NNPC) ya bayyana cewa ya samu ribar bayan haraji (PAT) na Naira biliyan 185 a watan Yuli.

A cikin sabon “Rahoton Watan Yuli 2025”, kamfanin ya ce wannan adadi ya ragu da kashi 79.56% idan aka kwatanta da Naira biliyan 905 da aka samu a watan Yuni.

NNPC ya ce raguwar ribar ta samo asali ne daga farashin kayan sayarwa da kuma gyaran harajin kuɗin shiga.

KU KUMA KARANTA: Kamfanin NNPC yakara farashin litar mai

Rahoton ya ce adadin ya ƙunshi jimillar kuɗaɗen shiga na rukunin kamfanin gaba ɗaya, ciki har da ma’amalolin cikin gida.

A cewar NNPC, fitar da danyen mai da ya kai matsakaicin ganga miliyan 1.7 a kullum a watan Yuli, yayin da samar da iskar gas ya kai miliyan 7.72 a kullum.

Leave a Reply