Kamfanin NNPC yakara farashin litar mai
Daga shafaatu Dauda Kano
Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPC) ya ƙara farashin litar fetur zuwa Naira 915 a birnin Lagos, yayin da ake sayar da shi kan Naira 945 a birnin Abuja.
Wannan sabon farashi ya nuna ƙarin Naira 45 daga tsohon farashin Naira 870 a Lagos, da kuma ƙarin Naira 35 daga tsohon farashin Naira 910 a Abuja.
KU KUMA KARANTA: Kanfanin man NNPC ya rage farashin litar man fetur a Kano da Jigawa
Jaridar TheCable ta rawaito cewa wannan canjin ya fara a yau Litinin, inda aka tabbatar da sabon farashin Naira 915 a wasu gidajen man NNPC a Lagos.
A gidan mai na NNPC dake Fin Niger, Badagry Expressway, an sayar da man kan farashin Naira 915.
A birnin Abuja kuwa, an sayar da lita ɗaya na fetur kan Naira 945 a yankin Federal Housing, Kubwa, wanda ya haura daga tsohon farashin Naira 910.