Hukumomi a Saudiyya sun kama tabar wiwi a jakar wata ‘yar jihar Kano

0
199
Hukumomi a Saudiyya sun kama tabar wiwi a jakar wata 'yar jihar Kano

Hukumomi a Saudiyya sun kama tabar wiwi a jakar wata ‘yar jihar Kano

Daga Jameel Lawan Yakasai

Hukumomi a ƙasar Saudiyya na tsare da wata mata ‘yar jihar Kano, Maryam Hussaini Abdullahi, bayan da ake zargin kamfanin jirgin sama na Ethiopia, wato Ethiopian Airline ya musanya jakar ta da wata mai ɗauke da tabar wiwi.

Maryam ta tafi Saudiyya tare da mijinta, Abdullahi Baffa, don yin Umrah a ranar 6 ga Agusta, amma daga bisani aka tsare ta a Makkah bayan ƴansanda sun danganta ta da wata jakar “Ghana-must-go” cike da kayan da ake zargi na ƙwaya ne.

Mijinta, Abdullahi Baffa, ya ce sun tafi Saudiyya da matar sa kowa da jaka ɗaya, amma bayan isowarsu Jiddah, sai ba su ga nasu kayan ba.

A cewar Baffa, ya shigar da korafin batan jakunkunan nasu inda aka basu don su ka cike aka kuma ce su jira sai hakan awanni 24.

Sai ya ƙara da cewa sai da ya yi haniya daga bisani aka ce masa ai haka jaridar ta ke, inda daga nan su ka wuce Madinah su ka sayi wasu kayan na amfanin su a can.

KU KUMA KARANTA: Ƙasar Saudiyya ta saki ‘yan Najeriya 3 bayan tsare su tsawon watanni 10

“Bayan kwanaki 8, sai aka kira ni aka ce wai an ga daya daga ciki jakunkunan namu saboda haka mu je mu karba. Sai na ce musu kawai a aika Nijeriya ma karba a can,”

Baffa ya ce sun zo dawowa ne tun a filin jirgin sama na jeddah, bayan an kammala tantance shi sai aka ma’aikatan Ethiopian Airline su ka fada masa cewa an riƙe matar sa, sannan su ka ce ya je cibiyar kula da masu ta’ammali da miyagun kwayoyi ta Saudi Arebiya dokin karin bayani.

Ya ce daga nan ne ya tuntubi ofishin Jakadancin Nijeriya a Saudiyya inda ya samu taimakon da ya dace.

Ya zargi kamfanin jirgin da hada musu da wannan jaka ba tare da saninsu ba.

Baffa ya ce bayan sun shigar da korafi a Jiddah, sai daga baya aka sanar da shi cewa daya daga cikin jakunkunan ya iso, amma ya ki karba, ya nemi a mayar da shi Najeriya.

Baffa ya ce matarsa ta tabbatar masa cewa aka nuna mata jaka cike da kayan da ba ta san komai ba a kansu.

Ya yi zargin cewa kamfanin jirgin yana kokarin boye gaskiya kan lamarin. Ya kuma nemi gwamnatin Najeriya ta gaggauta shiga tsakani domin kubutar da matarsa.

Kamfanin jirgin na Ethiopian Airlines ya tabbatar da cewa an fara bincike kan lamarin, yayin da ofishin jakadancin Najeriya a Jiddah ya ce sun karɓi rahoton kuma bincike yana gudana.

Lamarin ya tunatar da na Zainab Aliyu a 2018, wacce aka tsare a Saudiyya bisa irin wannan zargi, kafin daga baya aka gano cewa ba ta da laifi.

Leave a Reply