Hukumar Hisbah a Yobe ta kama kwalaben giya, ta rufe gidajen Karuwai a Gashuwa

0
240

Hukumar Hisbah a Yobe ta kama kwalaben giya, ta rufe gidajen Karuwai a Gashuwa

Hukumar Hisbah ta jihar Yobe, ƙarƙashin jagorancin Dakta Yahuza Hamza Abubakar tare da haɗin gwiwar rundunar tsaro ta haɗin gwiwa Operation Haba Maza, ta gudanar da babban samame a garin Alƙali, unguwar Walawa da ke cikin ƙaramar hukumar Gashua.

Wannan aiki ya kasance wani mataki na musamman domin daƙile munanan ɗabi’u da aikata ayyuka marasa kan gado, waɗanda suke barazana ga kyawawan ɗabi’u da tsaron al’umma.
Da rahamar Allah, hukumar ta samu nasara mai girma a wannan aiki.

A yayin wannan samame, an ƙwace Giya mai tarin yawa da ta cika manyan motoci guda huɗu. Haka kuma, an cafke mata 84 waɗanda aka kama suna harkar karuwanci.

Dukkan gidajen da ake gudanar da irin wannan ayyuka marasa kan gado an rufe su bakiɗaya, yayin da dukkan waɗanda aka kama suke hannun hukumomin tsaro, kuma za a gurfanar da su a kotu domin a yi musu shari’a bisa doka ta Jihar Yobe.

KU KUMA KARANTA: Hukumar Hisbah a Yobe ta farfasa kwalaban giya 243 a Damaturu

Hukumar Hisbah ta nanata ƙudirorinta waɗanda suka haɗa da:

Inganta tarbiyya bisa koyarwar addinin Musulunci da al’adun gargajiya.

Daƙile karuwanci, caca, shan giya da kuma amfani da miyagun ƙwayoyi.

Kare darajar mata da yara.

Tabbatar da zaman al’umma cikin tsafta, adalci da mutuntaka.

Hukumar Hisbah ta yaba da irin goyon baya da Gwamnan Jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni, ke bayarwa a fannonin kuɗi, kayan aiki da ƙarfafa gwiwa, wanda hakan ya ƙarfafa hukumar wajen gudanar da aikinta na tsare ɗabi’a da walwalar al’umma.

Shugaban hukumar, Dakta Yahuza Hamza Abubakar, ya yi ƙira ga jama’a da su ci gaba da zama masu lura da bin doka tare da bayar da rahoton duk wani abin da ya shafi aikata miyagun ɗabi’u a cikin al’umma, domin haɗin kan jama’a da hukumomi shi ne ginshiƙin ci gaban jihar.

Leave a Reply