Adam A. Zango ya auri jarumar Kannywood Maimuna Musa

0
413
Adam A. Zango ya auri jarumar Kannywood Maimuna Musa
Adam A. Zango da amaryarsa Maimuna Musa

Adam A. Zango ya auri jarumar Kannywood Maimuna Musa

Daga Jameel Lawan Yakasai

Fitaccen jarumin masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Adam A. Zango ya angwance da jaruma Maimuna Musa.

Shugaban hukumar tace fina-finai da ɗab’i na Jihar Kano Abba El-Mustapha ne ya wallafa labarin auren nasu a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Inda yace Adam Zango Allah ya sanya alkhairi yabada zaman lafiya, tare da sanya hoton Ango da Amaryar a shafinnasa na Facebook.

Auren dai ya zo cikin bazata, domin babu wanda ya san da neman sai labari aka ji jaruman sun shiga daga ciki.

KU KUMA KARANTA: Fittaccen jarumin Kannywood Adam A. Zango Yayi Hatsarin mota

Jaruma Maimuna matashiya ce wadda tauraronta ya fara haskawa a Kannywood.

Ta yi fina-finai kamar Kwana Casa’in, Garwashi da sauransu.

A baya-bayan nan ma fitacciyar jaruma a masana’antar, Rahama Sadau, ita ma ta yi aure, lamarin da ya bai wa mutane da dama mamaki.

Leave a Reply