Haɗakar jam’iyyu ne kawai zai iya kayar da Tinubu ba ɗaiɗaikun mutane ba – Malam Ibrahim Shekaru
Daga Jameel Lawan Yakasai
Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jigo a jam’iyyar PDP, Malam Ibrahim Shekarau, ya jaddada cewa haɗakar jam’iyyu kai tsaye ita ce hanyar kawar da gwamnatin Tinubu a 2027 ba ta ɗaiɗaikun mutane ba.
Shekarau ya ce ba a fahimci maganganunsa na baya ba kan haɗakar wasu ƴan siyasa a karkashin jam’iyyar ADC domin kwace mulki daga hannun APC.
KU KUMA KARANTA: Jagoran PDP a Yobe, Adamu Waziri ya fice daga jam’iyar ya koma ADC
Ya bukaci dukkan jam’iyyun adawa da su binciko hanyoyi da dabarun farfaɗo da dandalin siyasa domin cimma wannan buri, inda ya bayar da misalin yadda shi da wasu ƴan kishin ƙasa suka yi ƙoƙarin kafa haɗaka a 2011 domin kifar da tsohon shugaba Goodluck Jonathan daga mulki.









