Dalilin da ya sa shugabannin Larabawa ke hana goyon bayan Falasɗinu – Masanin Gabas ta Tsakiya, Ramzy
Jagoran al’ummar Falasɗinu a Najeriya kuma manazarci a Gabas ta Tsakiya, Abu Ibrahim Ramzy, ya zargi shugabannin ƙasashen Larabawa da ƙin goyon bayan Falasɗinawa da kuma ƙin tofa albarkacin bakinsu kan kisan gillar da ake yi a ƙasar, saboda fargabar da suke da shi daga Isra’ila da Amurka, yana mai nuni da cewa za a kori akasarinsu daga kan karagar mulki idan suka bijirewa muradu da buƙatar Washington da Telaviv.
Da yake magana a wata hira ta musamman da manema labarai yayin wata ziyara ta musamman da ya kai kamfanin jaridar Neptune Prime ranar Litinin a babban ofishin yaɗa labaranta da ke Abuja, Mista Ramzy ya ce “mafi yawan waɗanda ake kira shugabannin Larabawa ba su wuce ‘yan amshin shatar Isra’ila da kawayenta ba, don haka galibi suna inganta muradin yahudawan sahyoniya da daular mulkin mallaka ga al’ummarsu da sauran Larabawa da ke wajen ƙasashensu.
KU KUMA KARANTA: Mutanen da Isra’ila ta kashe a Gaza sun ƙaru – Rahoto
Ramzy ya koka kan halin da ake ciki na ban tausayi da al’ummar musulmi kusan biliyan biyu a duniya ke ganin kamar ba su da ƙarfin ƙalubalantar zaluncin da ake ci gaba da yi a Falasɗinu musamman kisan kiyashin da Isra’ila ke yi a Gaza tun watan Oktoban 2023.
Yayin da yake yaba wa irin jaruntakar da Iran da Yemen suka yi na tsayawa tsayin daka a kan gwamnatin sahyoniya, Mista Ibrahim ya yi Allah wadai da munafuncin ƙasashen Larabawa da ke nuna suna goyon bayan Falasɗinu amma a zahiri suna ci gaba da fafutuka da muradun Isra’ila.
KU KUMA KARANTA: Isra’ila ta kashe Falasɗinawa 14 a sabbin hare-hare da ta kai a Gaza
Musamman ma ya zargi shugaban ƙasar Masar Abdel Fattah el-Sisi da ƙin bin ka’ida idan aka yi la’akari da yadda yake nuna ƙyama ga ‘yan gudun hijirar Falasɗinawa a ƙasarsa da kuma hana zirga-zirgar motocin ɗaukar kayan agaji kyauta ta kan iyakar Masar zuwa Gaza.
Mista Ramzy ya yabawa ƙasashen Najeriya, Ghana da sauran ƙasashen Afirka kan goyon bayan Falasɗinu a irin wannan mawuyacin lokaci a tarihin fafutukar da suke yi na yaƙi da mamayar da aka yi, da kisan kiyashi da kuma lalata ƙasar kakanninsu.
KU KUMA KARANTA: Isra’ila ta bai wa Falasɗinawan Gaza umarnin barin gidajensu – MƊD
Yayin da yake kira da a ƙara ƙaimi da kuma dorewar kokarin daga kasashen Afirka, Mista Ibrahim ya yaba da irin jajircewa da gagarumin goyon bayan da ƙasar Afirka ta Kudu ta samu wanda ya ce “ba shakka ya kasance ne saboda irin abubuwan da ƙasar ta samu a zamanin mulkin wariyar launin fata da kuma tsawon shekaru da dama na goyon bayan da Falasɗinu ta bayar ta hannun ƙungiyar ‘yantar da Falasdinu, (PLO)”.









