Zan ci gaba da yin takarar Gwamnan Kano har sai na yi nasara – Sheikh Ibrahim Khalil
Daga Jameel Lawan Yakasai
Ɗan takarar gwamnan Kano a jamʼiyyar ADC 2023, Malam Ibrahim Khalil ya ce zai ci gaba da yin takarar gwamna a jihar Kano har sai ya cimma burinsa.
Ya bayyana haka ne a zantawarsa da manema labarai, bayan da yan siyasa ke ci gaba da shiga jami’iyyar ta ADC.
KU KUMA KARANTA: Zan yi haɗaka da sabuwar jam’iyyar ADC don a kayar da Tinubu, amma ba zan fice daga jam’iyar PDP ba – Sule Lamiɗo
Sheikh Khalil wanda ya taɓa yin takarar gwamnan Kano sau ɗaya, da kuma takarar neman zama ɗan takara gwamna a baya, ya kasance cikin waɗanda suka fi samun ƙuri’u a zaɓen 2023, a bayan jam’iyyun NNPP da APC da kuma PDP.









