‘Yar jihar Yobe ta lashe gasar Turanci ta Duniya a Burtaniya
Nafisa Abdullah, ‘yar shekara 17 daga ‘yar asalin jihar Yobe, a Arewa maso Gabashin Najeriya, ta kafa tarihi inda ta zama zakara a duniya a fannin Turanci a babbar gasa ta fasahar harshen Turanci ta ‘TeenEagle’ na shekarar 2025 da aka gudanar a birnin Landan na ƙasar Birtaniya.
Nafisa ta fafata da sama da mahalarta 20,000 daga ƙasashe 69 na duniya, inda ta zama ta ɗaya a gasar ‘UK Global Finals’, inda ta zarce takwarorinta na ƙasashe da ke jin Ingilishi da sauran masu fafutuka a duniya. Gagarumin nasarar da ta samu ya haifar da alfahari a faɗin Najeriya, musamman a jiharta ta Yobe.
KU KUMA KARANTA: Gwarzon gasar Alƙur’ani ya kuɓuta daga hannun ’yan bindiga a Katsina
Ta wakilci Najeriya ta Kwalejin Tulip International College (NTIC), jihar Yobe, an yi bikin nasarar Nafisa ne sakamakon sadaukarwar da ta samu, da samun ingantaccen ilimi, da kuma yanayin da shugabannin jihar suka samar.

Ɗan’uwan gwarzuwar yarinyar mai suna Malam Hassan Salihu ya yabawa gwamnatin jihar Yobe bisa irin gudunmawar da ya bayar.
“Nasarar da ‘yar mu ta samu a duniya ba za ta yiwu ba idan ba tare da tallafin mai girma Gwamna Mai Mala Buni ga fannin ilimi a jihar Yobe,” in ji shi.
Ya kuma yabawa shuwagabanni da ma’aikatan koyarwa na NTIC bisa muhimmiyar rawar da suke takawa wajen tsara tafiyar karatun Nafisa.
KU KUMA KARANTA: Gwamnan Kano ya karrama zakarun gasar karatun Alƙur’ani, ya ba su kujerun aikin Hajji
Gwamna Mai Mala Buni, CON, wanda a kodayaushe ya baiwa ilimi fifiko a matsayin ginshiƙin ci gaba a jihar Yobe, ana yabawa matuƙa dangane da sauye-sauyen da ya ke yi da saka hannun jarin da yake yi a fannin ilimi, kuma hakan ya sa harkar ilimi ke samun karɓuwa a duniya.
Nasarar da Nafisa ta samu, musamman a fagen da ƙasashen da ke amfani da turancin Ingilishi suka mamaye shi, ya zama wata babbar shaida ga abin da matasan Najeriya za su iya cimma idan aka ba su dama da goyon baya.
A yayin da jihar da al’ummar ƙasar ke murnar nasarar da ta samu, jama’a da dama na yin kira da a sake ɗaura ɗamarar ganin an samu ci gaba a fannin ilimi tare da jaddada cewa da irin jagoranci mai hangen nesa irin na Gwamna Buni, ɗaliban Najeriya za su iya yin fice da kuma yin takara a matsayi mafi girma a duniya.









