Sayyid Khamene’i ya sake naɗa manyan Malamai 3 a majalisar tsaron Iran
A ranar Talata, Jagoran Juyin Juya Hali na Iran, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei, ya sake naɗa Ayatollah Alireza Arafi, Ahmad Khatami, da Ahmad Hosseini-Khorasani a matsayin membobin limamai (faqihai) na Majalisar Tsaro (Guardian Council).
Wannan majalisa mai mambobi 12 na da muhimmiyar rawa a tsarin mulkin Iran, tana tantance dokoki, tace ‘yan takara, kuma tana kula da ingancin zaɓe. Jagora yana naɗa limamai 6, sannan sauran 6 masu ilimin doka ne daga bangaren shari’a da majalisa ke amincewa dasu.
KU KUMA KARANTA: Ministan tsaron Saudiyya ya gana da shugaban addini na Iran Khamenei, ya miƙa masa wasiƙar Sarki Salman
Ga bayanan wanda aka naɗa ɗin:
Alireza Arafi, Shugaban makarantu na addini (Hawzah) a Iran da limamin Jumma’a na Qom.
Ahmad Khatami, Limamin Jumma’a na Tehran wanda ke wakiltar Kerman a Majalisar Masana.
Ahmad Hosseini-Khorasani, Malami daga Qom mai ƙwarewa wajen haɗa ilimin addini da tsarin doka, wakilin Razavi Khorasan a Majalisar Masana.
Jagoran ya bayyana cewa sake naɗin yana da nufin dorewar tsarin da ke kare tsarin mulkin Musulunci a Iran.









