Gwamnatin Kano ta yi watsi da sabon Asibitin Kwanar Ɗangora – Mazauna Ƙiru da Bebeji

0
424
Gwamnatin Kano ta yi watsi da sabon Asibitin Kwanar Ɗangora - Mazauna Ƙiru da Bebeji

Gwamnatin Kano ta yi watsi da sabon Asibitin Kwanar Ɗangora – Mazauna Ƙiru da Bebeji

Daga Jameel Lawan Yakasai

Ƙungiyar ci gaban yankin Ƙiru da Bebeji sun koka bisa halin ko’in kula da suka ce gwamnatin jihar Kano ta ke yi na ƙin buɗe sabon Asibitin Kwanar Ɗangora.

Duk da cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ƙaddamar da takararsa ta 2023 a wannan garin na KWANAR ƊANGORA, Gwamna Abba ya sha alwashin kawo gyare gyare a mulkinsa amma wannan gari ya kasa samun kulawar Gwamna Abba duk da gatan da wannan garin ya yi masa.

Wannan sabon Asibiti (KAFIN MAIYAKI COTTAGE HOSPITAL) Sen. Rabiu Kwankwaso ne ya fara assa shi wanda gwamnatin da ta gaje shi tayi iya kokarinta wajen kammalawa amma hakan baiyiwu ba sai a wannan gwamnatin ta Alh. Abba ta karasa, kusan kashi 99% an kammala amma har yanzu ba a buɗe shi ba, wanda hakan ya haifar da fushin al’umma, inda suke zargin kwamishinan lafiya da hana aiwatar da manufar gwamnan.

Idan ka baro Zaria ba wani babban Asibitin sai ka zo Kura kuma kusan kullum ana samun hatsari wanda rashin asibitin kan haifar da rasa rayuka.

Marasa lafiya na kwanciya a wurare marasa lafiya da mutunci, musamman idan an samu hatsari a yayin da asibitin da ya kamata ya taimaka su ke ci gaba da zama a rufe. Alamu na nuna cewa kwamishinan lafiya na iya bata wa gwamnati suna a idon al’umma bisa gazawarsa na isar da sakon al’umma ga Gwamnati.

Al’umma sun bayyana cewa idan wannan matsala ba ta sami mafita ba, a 2027 insha Allah za su nuna fushinsu ta hanyar kada kuri’a ta sauya gwamnati, wanda ba burinmu kenan ba.

Leave a Reply