Ɗaliban Sakandire a Sakkwato sun ƙera mota mai amfani da lantarki
Daga Shafaatu Dauda Kano
A wani ci gaba mai ban mamaki da ya ja hankalin ƙasa baki ɗaya, ɗaliban makarantar Brilliant Footsteps International Academy da ke jihar Sakkwato sun ƙera mota mai amfani da lantarki, abin da ke zama babban ci gaba a fannin ilimi da fasaha a Najeriya.
An sanya wa motar suna BMT 1.0, inda ƙungiyar dalibai 15 ’yan ajin ƙarshe (SS3) suka ƙirƙira, suka tsara kuma suka haɗa motar gaba ɗaya. Daliban sun haɗa da mata goma da maza biyar, kuma aikin ne na ƙarshe kafin kammala karatun su.
Wani Rahoto ya bayyana cewa wannan aiki na farko irinsa daga daliban sakandare a Arewacin Najeriya yana kara haskaka burin Najeriya na dogaro da kai a fannin kere-kere, dorewar ci gaba da kuma ’yancin masana’antu.
KU KUMA KARANTA: Hisbah a Kano za ta fara kamen masu hira da mata a cikin mota
“Wannan ba kawai aikin makaranta ba ne saƙo ne,” in ji Dr. Shadi Sabeh, mai makarantar, a lokacin da aka bayyana motar a bainar jama’a.
Shugaban ƙungiyar ƙirƙirar motar, Ahmed Sadi, ya bayyana cewa sun gudanar da aikin kamar ƙungiyar injiniyoyi mai girma. “Kowane ɗalibi na da aikin da yake yi, daga walda, haɗa igiyoyin wuta, shigar da batir har zuwa gwajin tuki. Mun koyi aikin ta hanyar aikatawa,” in ji shi.
Daya daga cikin jagororin aikin, Aisha Ahmed, ta bayyana da kwazo da hangen nesa cewa tana cewa wannan mota hujja ce cewa kere-kere na iya faruwa a wuraren da ake rainawa. Idan aka ci gaba da wannan aiki kuma aka inganta shi, zai rage dogaro da Najeriya ke yi da shigo da motoci daga ƙasashen waje, tare da ƙarfafa sufuri mai ɗorewa.”









