Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya fice daga PDP
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, GCON, ya fice daga jam’iyyar PDP a hukumance ba tare da ɓata lokaci ba, saboda “bambance-bambancen da ba a daidaita ba” da yadda jam’iyyar ke tafiya a halin yanzu. Inji shi.
A wata takarda mai ɗauke da kwanan watan 14 ga watan Yuli, 2025, ga shugaban jam’iyyar PDP, Jada 1 Ward, Jada LGA, jihar Adamawa, Atiku ya bayyana matuƙar jin daɗinsa kan damammakin da jam’iyyar ta ba shi.
KU KUMA KARANTA: Haɗakar Atiku, El-Rufa’i da Obi ba zai iya kayar da APC ba a 2027 – Shekarau
Yin hidimar cikakken wa’adi biyu a matsayin mataimakin shugaban Najeriya da zama ɗan takarar shugaban ƙasa sau biyu yana ɗaya daga cikin abubuwa muhimmai a rayuwata,” ya rubuta a takardar.
Atiku, wanda yana cikin waɗanda suka kafa jam’iyyar PDP, ya bayyana yin murabus ɗinsa a matsayin abin takaici. Duk da haka, ya ce, “Na ga ya zama dole in raba hanya saboda yanayin da Jam’iyyar ta ɗauka a halin yanzu, wanda na yi imanin ya bambanta da ƙa’idojin da muka tsaya a kai.”
Ya ƙara da cewa, “Da baƙin ciki ne na yi murabus, tare da fahimtar bambance-bambancen da ba a daidaita su ba da suka kunno kai.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya yi fatan alheri ga jam’iyyar da shugabanninta a nan gaba. Shugaban jam’iyyar na yankin ya karɓi takardar kuma ya amince da shi a wannan rana.









