An yi jana’izar tsohon Sanatan Yobe ta Kudu, Adamu Talba a Nangere

0
268
An yi jana'izar tsohon Sanatan Yobe ta Kudu, Adamu Talba a Nangere
Ana yiwa Sanata Adamu Talba Sallar jana'iza

An yi jana’izar tsohon Sanatan Yobe ta Kudu, Adamu Talba a Nangere

An yi jana’izar Sanata Adamu Garba Talba a Sabon Garin Nangere a yau Talata. Babban limamin Masarautar Tikau Imam Uwaisu Idris ne ya jagoranci yi masa sallar jana’iza, a fadar mai martaba Sarkin Tikau da ke Sabon Garin Nangere, a ƙaramar hukumar Nangere ta jihar Yobe.

Marigayi Sanata Adamu Talba, wanda ya wakilci Yobe ta Kudu (Zone B) a majalisar dattijai, daga 2007 zuwa 2011. Ya rasu ne a Asibitin ƙasa da ke Abuja a ranar Litinin 14 ga Yuli 2025, bayan gajeriyar rashin lafiya. Ya rasu yana da shekaru 73, ya bar mata ɗaya (1) da ‘ya’ya biyar (5).

KU KUMA KARANTA: Sanata Ibrahim Bomai ya ƙaddamar da shirin bayar da tallafin karatu don inganta ilimi a Yobe ta Kudu (Hotuna)

Mataimakin gwamnan jihar Yobe Hon. Idi Barde Gubana (Wazirin Fune) ya halarci Sallar Jana’izar Marigayi Sanata Adamu Garba Talba (Magajin Garin Tikau). A jawabin da ya yiwa manema labarai jim kadan bayan jana’izar, mataimakin gwamnan, ya bayyana marigayin a matsayin ɗan siyasa mai tawali’u, jajircewa kuma mai karamci wanda ya shahara kuma mabiyansa ke so.

Mataimakin gwamnan ya samu rakiyar mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Yobe, Hon Ya’u Usman Dachiya da ‘yan majalisar dokokin jihar da kwamishinoni da masu ba da shawara na musamman.

Sauran waɗanda suka halarci jana’izar sun haɗa da Sarkin Fune da Sarkin Pataskum da kuma dubban al’umma a jihar Yobe da kewaye.

Mataimakin gwamnan a madadin sa da gwamnatin jihar Yobe ya jajantawa iyalan marigayin, sarki da mutanen ƙaramar hukumar Nangere da kuma shiyyar Yobe ta Kudu (Zone B).

Ya kuma jajanta masa tare da addu’ar Allah ya jikan marigayin, ya kuma baiwa iyalansa hakurin rashinsa. Ya kuma yi addu’ar Allah ya saka masa da Aljannatul Firdausi.

Leave a Reply