Farashin kayan abinci ya sauƙa sosai ,amma takin zamani ya fi ƙarfinmu – Manoma

0
330
Farashin kayan abinci ya sauƙa sosai ,amma takin zamani ya fi ƙarfinmu – Manoma
Takin zamani

Farashin kayan abinci ya sauƙa sosai ,amma takin zamani ya fi ƙarfinmu – Manoma

Daga Shafaatu Dauda Kano

Wani mai sayar da shinkafa kuma manomi a garin Danhassan da ke karamar hukumar Kura a jihar Kano, ya bayyana jin dadinsa dangane da faduwar farashin shinkafa a baya-bayan nan, yayin da kuma ya koka da tsadar takin zamani.

Yace hakan ya na barazana da aniyarsu na samar da abinci ga arewacin Najeriya.

Manomin mai suna Aminu, a wata hira ta musamman da Jaridar NEPTUNE PRIME ta Wayar Salula ya ce farashin shinkafa ya ragu matuka idan aka kwatanta da bara, wanda hakan ya janyo masu karamin karfi suka samu rangwame.

Shinkafar girki ta yau da kullun ana sayar da ita akan naira 2,500 kowane mudu, sai shinkafar tuwo mai kyau suna sayar da ita naira 2,900.

Manomin yace irin wannan shinkafar ta tuwo a shekarar data gabata ana sayar da ita ne naira dubu 4000 zuwa 4,200 kwano daya.

Sai dai duk da karyewar farashin shinkafar manomin ya nuna damuwarsa kan tsadar takin da ya ce manoma da dama ke da wuyar iya jurewa wajen sayansa.

A cewarsa, farashin takin Urea ya tashi lokaci daya daga naira 35,000 zuwa naira 40,000 kowanne buhu, al’amarin da ya bayyana a matsayin abin takaici, musamman ga kananan manoma da tuni suka shuka amfanin gona kuma suke kokawa akai.

Baya ga Urea, Aminu ya ce takin NPK wanda yake da mahimmaci a noman shinkafa yanzu ana siyar da shi tsakanin naira 55,000 zuwa naira 58,000 wanne buhu ya danganta da Inda za’a kaiwa mutum.

Ya yi kira ga gwamnati a dukkan matakai da su gaggauta shiga tsakani ta hanyar bayar da tallafin kudi ko takin zamani ga manoma domin ganin an ci gaba da samar da abinci tare da samun saukin a Najeriya a bangaren noma.

NEPTUNE PRIME ta rawaito cewa a ranar 29 ga watan Yuni da ya gabata ne gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da rabon takin zamani ga manoma a Kano a kokarin saukakawa manoman.

Kowacce karamar hukuma a Kano ta samu babbar motar tirela guda uku mai dauke da buhun takin guda 600.

Gwamna Yusuf yace gwamnatinsa ta rage kaso 50 cikin 100 na kuɗin takin ga manona domin saukaka musu,Inda gaba daya takin da aka rabar ya kama buhu dubu 79,200.

Leave a Reply