Kisan gilla a Mangu, an gurfanar da mutane 20 a kotu a Jos

0
156
Kisan gilla a Mangu an gurfanar da mutane 20 a kotu a Jos

Kisan gilla a Mangu an gurfanar da mutane 20 a kotu a Jos

Daga Idris Umar Zariya 

A ranar Jumma’a, Babbar Kotun Jihar Filato da ke Jos ta fara sauraron shari’ar mutane 20 da ake zargi da hannu a mummunan kisan mutane 13 da ya auku a ranar 20 ga Yuni, 2025, a kauyen Mangun da ke karamar hukumar Mangu.

An gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu a ƙarƙashin shari’a mai lamba PLD/J115/2025, inda ake tuhumar su da laifuka hudu masu nauyi: hadin baki don aikata laifi, lalata da wuta da makamai masu haɗari, da kisan kai, wanda ya saba da tanade-tanaden Dokar Hukunta Laifuka ta Jihar Filato ta 2017 — Sassa na 59, 220, 313 da 189.

KU KUMA KARANTA: Ƙungiyar kare ‘yancin Musulmi ta MURIC, ta soki kwamitin da gwamnatin Filato ta naɗa don warware rikicin Mangu

Sunayen Wadanda Aka Kashe:

A cewar tuhumar da aka karanta a gaban kotu, an bayyana cewa wadanda ake zargin sun kai hari ba tare da wani dalili ba, suka kona motar haya mai zama 18 dauke da matafiya, tare da kashe mutane 13 kamar haka:

Aminu Samaila, Abdullahi Abdulwahab, Isa Abubakar, Malam Sani, Ibrahim Sani, Ramatu Danladi, Adamu Sani, Ma’awe Habibu, Alhaji Mukhtari Ahmad, Sani Abdullahi, Hamisu Danladi, da Baba Sani Hamisu.

Sunayen Wadanda Ake Tuhuma:

Rabiu Haruna, Julius Abaris, Clement Machel, Gideon Istifanus, Bamkat Dan’doka, Dauda Ezekiel, Lawrence Samaila, Mantu Daniel, Gabriel Sunday, Steven Luka, Joel Danladi, Plankat Ayuba, Nanfan Habiba, Frances Augustine, Andy Danladi, Gungret Appolos, Bamshak Letak, Titus Bakwet, Balmun Helon, da Chutse Salvation.

Dukkansu sun bayyana a kotu kuma sun musanta laifukan da ake tuhumar su da su.

Gudanar da Shari’a:

Lauyan gwamnati, Barr. Samuel I. Ikutanwa, ya nemi kotu da ta ba da damar ci gaba da shari’a ta hanyar tsara lokaci (case management), tare da bayar da umarnin tsare wadanda ake zargi a gidan gyaran hali na Jos.

Lauyan kare su, Babban Lauya Garba Pwul (SAN), bai ki amincewa da hakan ba, amma ya nemi beli ga wadanda ake tuhuma. Sai dai lauyan gwamnati ya ce doka ta ba su kwanaki bakwai don su amsa buƙatar belin, kuma kotu tana gab da shiga hutu.

Mai shari’a, Justice Boniface Ngyong, ya yanke hukunci cewa ba za a saurari buƙatar belin a wannan lokaci ba, amma ya shawarci lauyan me kare su da ya nemi beli a gaban alkalin hutu.

An daga sauraron shari’ar har zuwa 13 ga Oktoba, 2025, tare da bayar da umarnin cigaba da tsare wadanda ake tuhuma a gidan gyaran hali na Jos.

Leave a Reply