FUGA ta karrama Gwamnan Yobe da mutane 5 da digirin girmamawa
Gwamnatin tarayya dake Gashuwa ta karrama Gwamnan jihar Yobe Alhaji Mai Mala Buni CON da wasu mutane 5 da digirin girmamawa. Taron ya gudana ne a ranar Asabar harabar jami’ar da ke Gashuwa a Jihar Yobe.
Waɗanda aka ba wa Digirin girmamawan sun haɗa da Gwamna Buni na Yobe, uwargidan shugaban ƙasa Sanata Oluremi Tinubu, ministan harkokin ‘yan sanda, Sanata Ibrahim Gaidam, tsohon shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan Ibrahim, Sarkin Lafiya Alhaji Sidi Mohammed Bage da tsohon shugaban ma’aikata na tarayya Alhaji Bukar Goni Aji.
A jawabin da ya gabatar a wajen, Gwamna Buni ya jaddada muhimmancin ilimi ga ci gaban ƙasa.

KU KUMA KARANTA: Ɗangote ya ware Naira Biliyan 15 domin bunƙasa Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Ɗangote da ke Wudil
Ya bayyana cewa, “Tun da daɗewa, ilimi ya kasance wani muhimmin al’amari na ci gaba. Barrack Obama, tsohon shugaban ƙasar Amurka, ya ce “ilimi shine kuɗin tattalin arziƙin yau”.
“A jihar Yobe, abin baƙin cikin da muka samu shi ne matsalar rashin tsaro na Boko Haram ya kawo cikas a fannin ilimin tare da mummunan sakamako, ilimi ya fi fama da matsalar rashin tsaro, an lalata makarantu da dama, an kashe malamai da ɗalibai, an yi yunƙurin tayar da tarzoma ne da gangan don sanya ilimin yammacin duniya ya zama marar kyau da kuma rashin ci gaba.
“A bisa ƙudurinmu na sauya lamarin, na ayyana dokar ta-ɓaci kan ilimin Firamare a ranar farko da na hau kujerar Gwamnan Jihar mu a ranar 29 ga Mayu, 2019 tare da himma sosai wajen gyarawa da kuma ƙarfafa fannin.
“Don cimma wannan buri, gwamnatinmu ta ƙara wa ɓangaren ilimi kasafin kuɗi domin baiwa ma’aikatun ilimi da kimiyya da fasaha da na ilimi na farko da na sakandare damar aiwatar da ayyuka da kuma aiwatar da tsare-tsare kan ilimi yadda ya kamata.

Ya ƙara da cewa “Na yi farin cikin bayyana muku irin tsayin daka da ƙudurin da gwamnati da al’ummar jihar Yobe suka baje domin neman ilimi cikin himma.”
Gwamnan ya ce karramawar za ta ƙara zaburar da waɗanda aka karrama su ci gaba da yi wa jama’a hidima domin inganta ilimi.









