JAMB ta ayyana maki 150 a matsayin mafi ƙaranci na shiga jami’a a Najeriya

0
343
JAMB ta ayyana maki 150 a matsayin mafi ƙaranci na shiga jami'a a Najeriya

JAMB ta ayyana maki 150 a matsayin mafi ƙaranci na shiga jami’a a Najeriya

Daga Jameel Lawan Yakasai

Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Jami’o’i ta Ƙasa (JAMB) ta sanya makin 150 a matsayin mafi ƙanƙanta ga ɗalibai don shiga jami’o’i a ƙasar nan.

JAMB ta yanke wannan shawara ne a ranar Talata yayin Taron Tsare-tsaren Shiga Makarantu na 2025 da aka gudanar cibiyar taro ta kasa da ke Abuja.

Hukumar ta bayyana cewa mafi karancin maki ga kwalejojin koyar da aikin jinya shi ne 140, kwalejojin noma 100, sannan kuma kwalejojin ilimi 100.

“An kayyade mafi ƙarancin makin da za a yarda da shi wajen karɓar ɗalibai a zangon karatu na gaba da 150 ga jami’o’i, 100 ga kwalejojin fasaha (polytechnics), 100 ga kwalejojin ilimi, da kuma 140 ga kwalejojin koyar da aikin jinya, bisa amincewar shugabannin manyan makarantu,” in ji JAMB a shafinta na X.

Leave a Reply