Fitaccen Malamin addini Sheikh Dahiru Bauchi ya cika shekara 101 a duniya
Daga Jameel Lawan Yakasai
A yau fitaccen malamin Musulunci kuma jagoran mabiya Ɗarikar Tijjaniyya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya cika shekaru 101 da haihuwa.
An haifi Sheikh Dahiru Usman Bauchi ne a ranar 2 ga watan Muharram a shekara ta 1346 Hijira wanda a yau yake cika shekaru 101 cif a duniya.
KU KUMA KARANTA: Boko shirme ne, ku koyi aikin tela da tuƙu, inji Gwamnan Bauchi
Sheikh Dahiru masanin Al-Ƙur’ani ne, kuma ya shafe sama da shekara 40 yana gabatar da Tafsirin Alkur’ani a watan Ramadan.
Mashahurin malamin ya sadaukar da rayuwarsa wajen koyar da addinin Musulunci a Najeriya.









