Babbar Sallah: Farashin kayan miya ya yi tashin gwauron zabi a Kano

0
146
Babbar Sallah: Farashin kayan miya ya yi tashin gwauron zabi a Kano

Babbar Sallah: Farashin kayan miya ya yi tashin gwauron zabi a Kano

Daga Jameel Lawan Yakasai

Yayin da al’ummar Musulmi ke shirin gudanar da bukin Babbar Sallah a bana, hauhawar farashin kayan abinci, musamman kayan miya, na kara jefa jama’a cikin damuwa a Jihar Kano.

Binciken da wakilin Jaridar Neptune Prime ya gudanar a kasuwar Garu da ke Karamar Hukumar Madobi ya nuna cewa farashin kayan miya irin su tattasai, tumatir da attarugu ya tashi fiye da kima – abin da ke kara dagula rayuwar masu sayayya da ke fama da matsin tattalin arziki.

A ranar Lahadi da ta gabata, kwandon tattasai ya tashi daga Naira 28,000 zuwa Naira 34,000 cikin rana daya, yayin da tumatir ya haura daga Naira 11,000 zuwa Naira 15,000. Attarugu kuwa ana sayar da kwandonsa tsakanin Naira 38,000 zuwa Naira 40,000.

Wani dillalin kayan miya a kasuwar, Malam Sammani Zakari Ya’u, ya bayyana cewa hauhawar farashin ba ya rasa nasaba da karancin wadataccen kaya da kuma yawaitar bukata daga jama’a. A cewarsa, “Wannan tattasai daga Jihar Katsina ne muka samo shi, domin wanda ake nomawa a Kano ya kare. Kuma tun da kayan miya ba za a iya girki ba tare da su ba, dole ne a samo su daga nesa.”

KU KUMA KARANTA: Karyewar Farashin Kayan Abinci: Ba mu shigo da kayan abinci daga waje ba — Minista

Ya kara da cewa: “Tumatir tun da fari ana sayarwa Naira 10,000, amma lokacin da kasuwa ta cika da masu saye, farashin ya haura zuwa Naira 14,000. Attarugu kuwa tun tuni ya tashi. Gaskiya lamarin yana tayar da hankali.”

Haka kuma wata mai sayayya a kasuwar, Hajiya Khadija Aminu, ta bayyana damuwarta kan yadda farashin ke hauhawa cikin gaggawa. Ta ce: “Kwanan nan ana sayar da kwandon tumatir tsakanin Naira 3,500 zuwa Naira 4,000, amma yanzu sai ka biya Naira 12,000. Tattasai kuma daga Naira 7,500 ya haura zuwa Naira 30,000 ko fiye da haka. Wannan abu ya kamata gwamnati ta sanya ido a kai.”

A duk lokacin da ake gab da bukukuwan Sallah, musamman Babbar Sallah, irin wannan hauhawar farashi na kara ta’azzara – ba kawai a bangaren dabbobi ba, har da kayan girki da sauran kayayyakin masarufi.

Al’umma na ci gaba da kira ga gwamnati da masu ruwa da tsaki da su dauki matakan da za su rage radadin matsin rayuwa, musamman ga talakawa da ke bakin kokarinsu wajen gudanar da ayyukan sallah cikin kwanciyar hankali.

Leave a Reply