WhatsApp zai daina aiki a kan iPhone 6, Galaxy S4 da wasu wayoyin guda 11
Daga Jameel Lawan Yakasai
Daga 1 ga Yuni, 2025, kamfanin WhatsApp ya sanar da dakatar da aiki a kan wasu tsoffin wayoyi, ciki har da iPhone 6 da Galaxy S4, saboda karin tsaro da kuma sabbin hanyoyin aiki da sabunta manhaja.
Wata kafa ta rawaito cewar wannan mataki na daga cikin kokarin kamfanin Meta — mamallakin WhatsApp — na ci gaba da inganta tsaro da aiki yadda ya kamata ga masu amfani da wannan manhaja.
Rahotanni daga ECONOMIC TIMES sun tabbatar da cewa wannan sabuntawa na nufin wayoyin da ke amfani da tsofaffin tsarin aiki (Operating System) ba za su sake samun damar amfani da WhatsApp ba.
KU KUMA KARANTA: Yadda na yi wa budurwar da muka haɗu a Facebook yankan gunduwa-gunduwa — Matashi
Daga cikin wayoyin da WhatsApp ya daina aiki a kansu akwai:
iPhone 5s, iPhone 6, da iPhone 6 Plus, Samsung Galaxy S4 ,Sony Xperia Z1 ,Da wasu karin wayoyi 11 da ke amfani da tsohon tsarin aiki.
iPhone ta kasance tana da iOS 15.1 ko mafi sama yayin da Android ya kasance a kalla yana da Android 5.1 (wato Lollipop ko sama)
Wayoyin da ba su dace da wannan bukata ba za su iya gudanar da aikace-aikacen WhatsApp ba, wanda hakan zai hana su tura sako, kiran murya da bidiyo, ko amfani da sashen Status.
Kamfanin Meta ya bukaci masu amfani da waɗannan tsoffin wayoyin da su:
Sabunta tsarin wayarsu zuwa sabon sigar da ake bukata, idan hakan zai yiwu.
Ko kuma su koma amfani da sabbin wayoyi domin ci gaba da amfani da WhatsApp ba tare da matsala ba.
Meta ta kara da cewa ba za ta iya ci gaba da goyon bayan na’urorin da ke amfani da tsohon tsarin aiki ba, domin hakan na hana ci gaban fasaha da kuma hana aiwatar da sabbin fasaloli na manhajar kamar karin matakan tsaro da sabbin zaɓuɓɓukan Group da Status.
Domin tantance tsarin wayarka:
iPhone: Bude Settings, danna General, sannan About. Idan tsarin bai kai iOS 15.1 ba, WhatsApp ba zai sake aiki ba bayan 1 ga Yuni.
Android: Bude Settings, shiga About Phone, sannan duba tsarin Android. Idan bai kai Android 5.0 ba, WhatsApp zai daina aiki.