No menu items!

Sample Page Title

Date:

Najeriya ka iya zama kamar China idan aka koma tsarin jam’iyya daya – Ganduje

Daga Shafaatu Dauda Kano

Shugaban jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya, Abdullahi Umar Ganduje ya ce samun jam’iyyu barkatai na dagula tafiyar da gwamnnati a tsarin dimokraɗiyya.

Abdullahi Ganduje ya shaida hakan ne bayan ganawa da Shugaba Tinubu tare da wasu ƴan majalisar PDP da suka koma APC.

Shugaban, ya ce idan duka jam’iyyun siyasar ƙasar za su narke su koma APC, suna maraba da hakan.

”Yanzu idan ka duba ƙasar China tsarin jam’iyya guda suke bi, amma yau ƙasar China jagora ce a duniya wajen samar da ci gaban al’ummarsu”.

KU KUMA KARANTA: Kwankwaso da Ganduje ku haƙura da rikicin siyasar nan haka domin ci gaban Kano – Kashim Shettima

Ganduje ya ce idan ƴan Najeriya suka buƙaci komawa tsarin jam’iyyar guda, ba wanda zai yi faɗa da hakan.

Ƴanmajalisar Dattawan Najeriya uku na babbar jam’iyyar hamayya ta PDP daga jihar Kebbi za su sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC mai mulki, kamar yadda shugaban jam’iyyar APC na ƙasa ya tabbatar.

Sanatocin jam’iyyar PDP daga jihar Kebbi a yau sun tabbatar wa shugaban ƙasa cewa sun fice daga jam’iyyarsu ta PDP tare da dawo jam’iyarmu ta APC”, in ji Ganduje.

Abdullahi Ganduje ya ce sanatocin uku za su bayyana wa majalisar dattawa matsayar tasu a mako mai zuwa kamar yadda kundin tsarin ƙasar ya tanadar.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...