Gwamnan Edo ya ziyarci Kano don jajantawa kisan mafarauta 16

0
260
Gwamnan Edo ya ziyarci Kano don jajantawa kisan mafarauta 16

Gwamnan Edo ya ziyarci Kano don jajantawa kisan mafarauta 16

Daga Ibraheem El-Tafseer

Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo ya kawo ziyarar jaje ga gwamnatin Kano da iyalan mafarauta 16 da ɓatagari su ka ƙone su har lahira a garin Uromi na jihar.

Da ya ke jawabi a gidan gwamnati, Okpebholo ya nuna kaɗuwa bisa lamarin, inda ya tabbatar da cewa 14 daga waɗanda su ka aikata kisan sun shiga hannu kuma za a tabbatar an yi wa iyalan wadanda aka kashe adalci.

KU KUMA KARANTA:Kotu ta yanke hukuncin kisa ga matar da ta kashe yarinya ‘yar shekara 8 a Kano

Shi ma gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi ƙira ga gwamnan na Edo da ya tabbatar da an hukunta waɗanda ake zargi.

Gwamna Yusuf ya yi ƙira ga gwamnatin tarayya da ta baiyana fuskoki da sunayen mutane da aka kama kan kisan gillar, inda ya buƙaci gwamnan Edo ɗin da ya tabbatar an biya diyya ga iyalan mamatan.

Leave a Reply