Kotu ta yanke hukuncin kisa ga matar da ta kashe yarinya ‘yar shekara 8 a Kano
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Babbar Kotun Jihar Kano ta yanke wa wata matar aure, Fadila Adamu, hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samun ta da laifin sace wata yarinya ‘yar shekara takwas tare da jefata a rijiya, wanda ya yi sanadiyyar mutuwarta.
Yayin yanke hukunci a ranar Juma’a, Mai shari’a Yusuf Muhammad-Ubale ya yanke cewa masu gabatar da kara sun gabatar da hujjoji masu karfi fiye da shakku, inda suka tabbatar da laifin matar na satar mutum da kuma kisan kai.
“Ina yanke wa wacce ake tuhuma hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda sace yarinyar da jefata cikin rijiya, wanda ya yi sanadiyyar mutuwarta,” in ji Mai shari’a Muhammad-Ubale.
KU KUMA KARANTA:NAFDAC ta buƙaci a zartar da hukuncin kisa kan masu fataucin ƙwaya
Lauyan masu gabatar da kara, Lamido Abba-Sorondinki, ya bayyana wa kotu cewa lamarin ya faru ne a ranar 14 ga watan Yuli, 2019, a unguwar Tudun Wada, Kano.
Ya bayyana cewa matar ta sace yarinyar ne misalin karfe 4:45 na yamma, sannan ta kaita gidanta da ke unguwar Sabuwar Gandu.
A cewar sa, wacce ake tuhuma ta yi wa ‘yar uwarta karya, tana mai cewa yarinyar ‘yar wata kawarta ce da ta tafi Ghana, kuma ta bukaci a ajiye ta har sai mahaifiyarta ta dawo.